Translate

Sunday, August 17, 2014

Yadda Shekarau da Kwankwaso Suka Lalata Siyasar Kano

28 ga Mayu, 2014

Dakta Rabi'u Musa Kwankwaso tare da Mallam Ibrahim Shekarau
Daga: Amir Abdulazeez

T
un a zamanin NEPU da PRP, duniya ta ke yi wa Jihar Kano kallon madubin siyasar Arewacin Najeriya. Wannan ya biyo bayan aiki tuƙuru da gwarazan ‘yan kishin ƙasa irinsu Mallam Aminu Kano suka yi wajen nema wa Jihar Kano irin wannan matsayi. Domin kuwa irin nagartaccen samfurin siyasar da su Marigayi Aminu Kano, Muhammad Abubakar Rimi, Dan Masanin Kano da sauran irinsu suka gudanar a wancan lokaci, ya taka muhimmiyar rawa wajen ɗaga darajar siyasar Kanon musamman a Arewacin Najeriya.

A wancan lokaci, Jihar Kano ta yi fice wajen zaɓen mutum ko jam’iyyar da ta ke so a kowanne irin mataki ba tare da tsoro, kwaɗayi ko maguɗi ba.

A shekarar 1979, Jihar Kano ta zaɓi jam’iyyar PRP duk kuwa da cewa NPN ita a ke yayi a Najeriya kuma ita ce jam’iyyar da ta fi kowacce ƙarfi. A shekarar 1983, an juya wa Muhammad Abubakar Rimi baya duk da cewa shi ne ya ke da mulki kuma a ka zaɓi Sabo Bakin-Zuwo duk da cewar bai fi  Rimin farin jini a karan kansa ko kuma sanin siyasa ba. A waɗannan  lokuta, duk ƙarfin mulkin ka, ba ka isa ka tilastawa mutane su yi irin siyasar da ka ke so ba, ko kuma ka murɗe mu su zaɓe ba. Ire-iren waɗannan abubuwa su suka sanya a ke sha’awar siyasar Kano a ko’ina a Arewa kuma ya sanya ta shahara a fadin Najeriya.

A shekarar 2003, siyasar Jihar Kano ta cigaba da kafa tarihi inda ta samu ƙarin matsayi daga madubin Arewacin Najeriya zuwa madubin siyasar Najeriya baki ɗaya. Wannan ya biyo bayan zaɓen Mallam Ibrahim Shekarau da kuma faɗuwar Injiniya Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso. A lokacin, an yi ikirarin cewar Shekarau ya ci zaɓe alhalin ba shi da ajiyayyar N100,000 inda ya kayar da Gwamna Kwankwaso mai ƙarfin mulki, kuɗi da alfarma. Duk Najeriya ba inda aka taɓa ganin haka a wannan lokacin sannan kuma bayan yin la’akari da lalcewar al’amuran zaɓe a ƙarƙashin gwamnatin Shugaba Obasanjo  a wannan shekara,  an yi ittifaƙin cewar, babu inda aka gudanar da sahihin zaɓe a duk Najeriya kamar a Jihar Kano. A wannan shekara, ba wai Gwamna Kwankwaso kadai ba, a’a, ‘yan majalisu da dama ma su ƙarfin kuɗi da mulki sun yi asarar kujerunsu. Duk da cewa akwai gagarumin tasirin Janaral Buhari a siyasar Kano a wannan lokaci, amma wannan shekara ta 2003 ita ta tabbatar wa da duniya cewar siyasar Jihar Kano ta na nan daram yadda aka santa duk da lalacewar da siyasar Najeriya ta yi. Wato kuɗin ka ko mulkinka ko maguɗin ka a Kano bai isa ya ba ka mulki ba ba tare da sahalewar talakawa ba.

Tun daga wannan lokaci, duk inda ka je sai ka ji ana cewa ai ba ka isa ka yi maguɗi ko ƙarfa-ƙarfa a Jihar Kano ba, saboda yanayin siyasar jihar ya fi ƙarfin a yi mata irin cin kashin da a ke yi a sauran jihohi.

Duk waɗannan abubuwa da na ke zayyanowa a yanzu sun zama tarihi, domin kuwa yanzu siyasar Kano ta lalace kuma ta dawo gama-gari irin ta ko’ina a Najeriya. Kai a taƙaice ma idan aka ci gaba a haka, to jihohi irin su Oyo, Edo, Imo, Nassarawa da Zamfara za su iya shan gaban Kano ta fuskar inganticciyar siyasa ta ra’ayi da ‘yanci.

Wannan lalacewar da siyasar Kano ta yi ba komai ba ne face laifin tsohon Gwamnan Kano Mallam Ibrahim Shekarau da kuma Gwamna mai ci yanzu, Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso, ko da yak e mu kanmu mabiya mun bayar da tamu gudunmawar. Mutane da dama su na da ra’ayin cewar, a tarihin Kano, ba a taɓa samun mutanen da suka ci moriyar siyasar jihar irin waɗannan mutane guda biyu ba, amma yau ga shi su ne suka fi kowa lalata ta da yi mata mummunar illa.

Kwankwaso da shekrau su ne suka share wa maguɗin zaɓe wajen zama a Kano kuma su ne suka assasa al’adar sanya jam’iyya da shugabanninta a cikin aljihu.

Ba wai ina nufin waɗannan mutane babu wata gudunmawa da suka kawo ga ci gaban Kano ba. A’a, kowannensu ya yi mulki kuma ya bar tarihi mai kyau dai-dai iyawarsa ta hanyar yin abubuwa nagartattu da suka shafi rayuwar jama’a. To amma sun yi amfani da mulkinsu wajen gina rundunar siyasarsu da tara magoya baya. Sannan kuma sun yi amfani da damar su wajen yin abin da zai ciyar da siyasar su da ta jam’iyyar su gaba kawai, amma sun lalata tsari da ginshiƙin siyasar Kano kuma da alama hakan bai dame su ba. Aiyyukansu sun nuna cewar bas u damu ba dan tarihin siyasar Kano ya lalace in dai ta su siyasar za ta ci gaba da haɓɓaka. A taƙaice dai, sun lalata tsarin da su suka fi kowa cin moriyarsa a Kano.

Lokacin da Kwankwaso ya zama gwamna a shekarar 1999, babu wani abu na nagarta da alfarma a zahiri wanda Dakta Abdullahi Umar Ganduje bai fi shi ba. Amma saboda tsaftar siyasar Kano a wancan lokaci, ba a murɗe masa zaɓen fidda gwani na PDP  an baiwa Gandujen ba. Amma lokacin da jagorancin PDP ya dawo hannun Kwankwaso, a shekarar 2007, shi kaɗai ya yi fatali da nagartattun ‘yan takara kusan guda bakwai waɗanda suka shiga zaɓe tare da shi, ya ɗauki takara ya bai wa Ahmad Garba Bichi.

Idan muka waiwayi Shekarau, a shekarar 2003, tsaftar siyasar Kano na wancan lokaci ta sa aka yarda cewar Ibrahim Little ya karya doka ta hanyar tsayawa takara ba tare da ya ajiye muƙaminsa na shugaban jam’iyya ba, kuma ba a kalli kuɗinsa, yawan jama’arsa ko ɗaurin gindin sa ba, aka karɓe takara aka ba shi duk da cewar ba shi da kuɗi ko wani ubangida a siyasance kuma ana ganin ma ba zai iya takarar ba. Amma a shekarar 2011, lokacin da jagorancin jam’iyyar ANPP ya ke hannun Shekarau, sai ya jingine matsayinsa na jagora, ya tsaya kai da fata sai an zaɓi abokinsa Mallam Salihu Sagir Takai, kuma ya dage a kan haka inda ya yi amfani da dukkan damar da ta ke hannunsa wajen cimma burinsa duk kuwa da cewar mafi yawan ‘yan jam’iyyarsa ta ANPP ba su yarda da zaɓin nasa ba.

Sakamakon waɗannan abubuwa da Kwankwaso da Shekarau suka yi a baya, yau an wayi gari saboda lalacewar siyasa a Kano, kowa tsoron tsayawa takarar gwamna a ƙashin kansa ya ke yi domin in dai ba gwamna ko jagoran jam’iyya mai ci ne ya tsayar da shi ba to wai ɓata lokacinsa ya ke yi. Kuma komai nagartarka, ba za a taɓa samar da yanayin da zaka iya wata takarar kirki da ɗan lelen gwamna ba.

Idan muka dawo ɓangaren zaɓe, Jihar Kano ba ta san mummunan maguɗin zaɓe da danniya ba sai  a kan Shekarau da Kwankwaso. Duk da cewa a lokacin SDP da NRC, mutane da yawa na da ra’ayin cewar an yi murɗiya a zaɓen gwamna tsakanin Injiniya Magaji Abdullahi da Gwamna Kabiru Gaya; to amma wannan ma wasan yara ne a kan abin da muke gani a yanzu.

Na farko dai, mafi yawan zaɓen cike gurbi da aka yi a ƙarƙashin mulkinsu ba su da inganci. Tun daga zaɓen cike gurbin ɗan majalisar Jihar Kano mai wakiltar ƙaramar hukumar Nassarawa a shekarar 2006, har zuwa zaɓen cike gurbi na ‘yan majalisun Kano ma su wakiltar Gaya da Garko da aka yi a shekarar 2013; akwai rashin inganci a cikinsu.

A shekarar 2007 ne, gwamnatin Mallam Shekarau ta shirya zaɓen ƙananan hukumomi mafi muni a tarihin siyasar Kano inda ƙiri-ƙiri a ka dinga musanya sunayen waɗanda aka sanar sun ci zaɓe a filin zaɓe da sunan abokan takararsu a can wani wajen daban ko a wani lokacin daban, wannan zaɓe ya yi muni ƙwarai da gaske kuma mu a wannan lokacin mun ɗauke shi a matsayin tsautsayi da ƙaddara wacce muke fatan ba za ta ƙara faruwa a Kano ba. Sai ga shi ƙasa da sati biyu da suka gabata, gwamnatin Kwankwaso ta shirya wani zaɓen mummuna irinsa wai da sunan ta rama abin da Shekarau ya yi mata. A wannan almara mai kama da zaɓe, an ayyana cewar jam’iyyar APC ta lashe dukkan kujerun kansiloli 484 da ciyamomi 44 a Kano. To yanzu, menene abin birgewa a nan a ce babu adawa ko ɗaya kuma bayan kowa ya san hakan ba zai yiwu ba a Kano?

Da alama dai an saka talakawan Kano a tsakiya ana wasan ƙwallon ƙafa da su. Wannan ya sa su su shiga rana su hau layi don zaɓar ra’ayinsu, sai kuma a faɗi sakamakon da aka ga dama, sannan wancan ma ya aikata irin hakan wai sannan ya ce ai ramawa ya yi. Talakawan Kano su ne abin ya ke ƙarewa a kansu kuma abin takaici wai shugabanninsu su ke mu su haka.

A lokutan mulkin Shekarau da Kwankwaso, babu wanda ya ke da ikon ya zama shugaban jam’iyyar da suke ciki sai wanda suke so kuma shugabannin jam’iyya ba su da wani ‘yancin kansu sai dai ra’ayin gwamnati domin ta mayar da su jami’anta. Idan mutum ya na takara da gwamna ko ɗan lelen gwamna, shugabanni ba za su zama alƙalai ma su adalci ba, ƙarara za su nuna maka kai ba ma ɗan jam’iyyar ba ne ko kuma ka ma yi laifi da ka tsaya takara da gwamna. Mu a da sai dai mu ji labarin irin wannan abin takaicin a wasu jihohin amma ba dai a Kano ba.

A dalilin haka, yau mun wayi gari, gwamnoni su suke nada shugabannin  jam’iyya kuma ba su da wani amfani. Da ka nemi shawararsu ma, gara ka tunkari gwamnan mai mulki kai tsaye domin aikinsa kawai su ke yi ba na jam’iyya ba. Ya kamata waɗannan jagorori su koyi darasin da tarihin siyasarsu ya koya mu su. Su tuna cewar sun samu dama kuma sun rasa ta.


A gaskiya duk da cewa Injiniya Kwankwaso da Mallam Shekarau sun bai wa Kano gudunmawa a gwamnatance amma kuma sun kawo tarnaƙi ga tsarin da ta hanyar sa ne kawai za a iya samun wasu irinsu su ɓullo su ma su bayar da tasu irin gudunmawar. Yadda tsarin siyasa ya fito da su aka sansu, jama’ar Kano suka karɓe su kuma har suka samu dama, to su ma su ƙyale adalci ya tabbata a tsarin domin kowa ya samu dama ba tare da tsangwama ba. Har yanzu akwai dama a hannunsu domin su ne suke haska fitilar siyasar Kano har gobe. Idan suka bari wannan dama ta suɓuce daga hannunsu cikin wannan yanayi ba tare da sun gyara ba, to tarihi ba zai taɓa yafe mu su ba domin kuwa ba za a dinga tunawa da su irin tunawar da ake yi wa Mallam Aminu Kano ba. Mallam Aminu Kano ya samu babbar damar sa ne wajen yin jagoranci, Shekarau da Kwankwaso sun samu damar yin mulki a gwamnatance da kuma jagoranci a siyasance baki ɗaya.


No comments:

Post a Comment