10 Ga Satumba, 2014.
DAWAKIN-TOFA: Siyasa ko Masifa?
Daga: Amir Abdulazeez
K
|
u yi m in afuwa idan kalmar ‘masifa’
da na yi amfani da ita a wannan sharhi ta yi tsauri da yawa. Amma magana ta
gaskiya, da wahala a iya amfani da wata kalmar
ba ita ba wajen kwatanta ko bayyana irin yanayin da masu juya akalar siyasar Dawakin-Tofa
suka sanya ta a ciki.
Kimanin sati uku da suka
gabata, wani bawan Allah da muka fara mu’amala da shi a shekarar bara ya tare
ni a gidan wani ɗaurin aure. Bayan mun gaisa, sai ya bani haƙuri bisa ƙauracemin
da ya yi na kwana biyu. Yace ya ƙauracemin
ne saboda dalili na siyasa, domin wai ya na tsoron kada waɗanda ya kira
iyayen gidansa na siyasa a Jam’iyyar APC ta Dawakin-Tofa su gane ya na mu’amala
da ni ko kuma mutane iri na, su saka ƙafar wando ɗaya da shi, wai tunda a
cewarsa da ni da jaridar da na ke wallafawa, ana yi musu kallon masu adawa da
Maigirma Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje da kuma
wasu masu juya akalar APC a Dawakin-Tofa.
Da farko dai na so na tsare shi
sai ya bayyana min abin da ni na yi ko jaridar wanda ya ke nuna ana adawa da Gandujen
ko kuma da su iyayen gidan nasa, to amma sai na ga hakan ɓata lokaci ne, ba
lallai ne in samu wata gamsuwa ba. Kawai sai na yi masa godiya , muka yi sallama,
muka rabu ina jin tausayinsa bisa wannan hali da aka saka shi ko kuma ya saka kansa a ciki.
Bayan ‘yan kwanaki da faruwar
wannan sai na haɗu da wani mai riƙe da muƙami a gwamnatin ƙaramar hukumar Dawakin-Tofa
ya na bayyana wa wani abokinsa (shi ma wani shahararraen ɗan siyasa) cewar
iyayen gidansa sun shaida masa cewar kada ya ƙara alaƙa da wannan abokin nasa,
idan ba haka ba zai ji a jikinsa. Waɗannan mutane biyu abokai ne shekara da
shekaru kuma tare suka yi makaranta amma duk da wannan, wai ba a tunanin cewar
wata hulɗar daban za ta iya haɗasu wadda ba ta siyasa ba. Kai in ma hulɗar
siyasa za su yi tare, to sai me? Wai yaushe siyasa ta koma gaba ne. Wanna
masifa da me ta yi kama?
Kwanakin baya aka dinga yaɗa
labari cewar Honarabul Kawu Sumaila, ɗan takarar Gwamnan Jihar Kano, ya kira
dukkan shugabannin mazaɓu na Jam’iyyar APC na ƙananan hukumomi 44 na Jihar Kano,
amma wai sai aka hana na Dawakin-Tofa zuwa. Abin haushi da kunya, na ƙananan
hukumomi 43 sun je amma ban da na Dawakin-Tofa.
Wannan ko mun ƙi ko mun so, saƙon da muke isar wa da duniya shi ne har
yanzu Dawakin-Tofa siyasar gaba, duhun kai da jahilci muke yi ko da kuwa hakan
ba gaskiya ba ne. Shin
suna tsammanin da haka za a taimaki takarar Gandujen? Yanzu idan Maigirma,
Dakta Ganduje ya kira shugabannin Sumaila suka ƙi zuwa, mu ‘yan Dawakin-Tofa ya
za mu ji a ranmu? Idan kuma Kawu Sumailan Allah Ya ba wa Gwamnan Kano, ya ake
tunanin zai ɗauki ‘yan Dawakin-Tofa misali? A siyasance don kana son wani, ba za ka yi
mu’amala da kowa ba kenan?
Ya kamata Maigirma Mataimakin
Gwamna ya tsawatarwa waɗannan
mutane masu kiran kansu muƙarrabansa ko kuma masu sawa da hanawa a jam’iyyar
APC ta Dawakin-Tofa, waɗanda su ake zargi da aikata irin waɗannan abubuwa. Idan kuma da yawunsa
da yardarsa suke yin hakan , to sai a yi mana bayani domin mu san yadda abin ya ke. Ita dai
gaskiya matuƙar ɗaci ne da ita, kusan kowa ba ya so a faɗa masa ita, amma idan
ya daure ya karɓe ta ya yi amfani da ita, sakamakon ta zai zamo masa mai zaƙi.
Akwai buƙatar mu tuna cewar,
shi goyon baya da haɗin kan jama’a, ba a samunsa ta ƙarfi, ana samunsa ne a siyasance ta hanyar kyautatawa da
laluma. Ko’ina sai ɓatawa Ganduje suna a ke yi da sunan tallata shi, kuma
wannan ba ƙaramar mummunar illa ba ce ga wanda ya ke neman Gwamnan Kano ba wai
Gwamnan Dawakin-Tofa, kuma a shekarar 2015 ba wai 2019 ba. Idan har muka ga shiru
ba a samu gyara ba ko kuma ba a tsawatar ba, to za mu ƙaddara cewar Maigirma Ganduje
shi ya ba su izinin duk wannan abu da suke yi.
Shi jagoranci da ɗaukaka, Allah
Ne Ya ke ba da su, don haka mun yarda waɗannan mutane tauraruwarsu ita ta ke
haskawa kuma lokacinsu ne, kuma su ne jagorori. To amma ya kamata su yi amfani
da wannan dama don su bar kyakkyawan tarihi ta hanyar kawo gyara da cigaba,
amma ba su dinga kama-karya, son zuciya tare da haddasa gaba a tsakanin jama’a
ba.
Haka kawai yanzu an ɗauko wani
salo, idan ka na neman wani muƙami na siyasa, sai a ce wai ai ba ka son Ganduje
don haka a yaƙe ka, ko kuma a ce Ganduje ba kai ya ke so ba, don haka wai aikin
banza ka ke, da kai da banza duk ɗaya, ba za ka ci ba. To ko an manta cewar Allah Shi ya ke bayar da
mulki? Duk wanda ya
ke kan wata dama a yanzu, akwai wanda ya kai shi idan ba Allah ba? To ya kamata a sani, Ganduje uba
ne, kuma mu a tunanin mu matsayinsa ya wuce a ce wai ya na son wane ko bay a
son wane. Ya kamata a ce kowa na sa ne, kai har wanda ma ba ɗan
jam’iyyarsa ba.
Dawakin-Tofa ƙaramar hukuma ce
mai ɗumbin tarihi da daraja ba ma a Jihar Kano ba, a’a har a Najeriya
baki ɗaya. Ta na daga cikin ƙananan hukumomi ƙirƙirar farko a Najeriya baki ɗaya
kuma ita uwa ce da ta haifo kuma ta raini wasu ƙananan hukumomi irin su
Bagawai, Tofa da Rimin-Gado. Amma abin takaici, yanzu dariya su ke mana suna
cewar muna ƙarƙashin siyasar mulkin-mallaka, siyasar rashin ‘yanci da tsoro da
danniya.
Wannan ƙaramar hukuma ba mallakin
wani ba ce, ta mu ce baki ɗaya kuma haƙƙin mu ne mu haɗu tare mu ga cewar mun ciyar da ita
gaba. Amma idan wani ko wasu suna ganin cewa Dawakin-Tofa mallakar su ce kuma za
su tilastawa mutane ta ƙarfin tsiya su yi abin da suke so, to ba kansu farau
ba, kuma sai mu ce mu su: ‘Allah Ya bada sa’a’, gas u ga ‘yan Dawakin-Tofar
nan, ai kowa ya san inda ya ke masa ciwo.
Mallam Amir shi ne
Mawallafin Jaridar Muryar Dawakin-Tofa kuma Co-ordinator na shirin Dawakin-Tofa
Development Programme.
26th March, 2014.
NAZARI AKAN KATOƁARAR DA JAM’IYYAR APC TA KE TAFKAWA A
DAWAKIN-TOFA
Daga: Amir Abdulazeez
Sau tari mutum shi ya kan yi wa kansa
mummunar illa ko dai yana sane da gangan ko kuma ba ya sane cikin
jahilci. Domin kuwa duk abin da ka ke yi a kowanne lokaci ya na da gagarumin
tasiri a kan duk abin da zai sameka a yanzu ko kuma a wasu shekaru masu zuwa.
Lokacin da masu ruwa da tsakin tsohuwar jam’iyyar PDP Kwankwasiyya suka
dinga zagayawa mazaɓun ƙaramar hukumar Dawakin-tofa suna tara mutane tare da
neman goyon bayansu ta hanyar bayyana musu irin zalunci da kama karyar da uwar
jam’iyyarsu ta PDP ta ƙasa a wancan lokaci ta ke yi musu tare da jagororinsu,
da yawa daga cikin jama’a sun ɗauka da gaske suke yi, gyara suke nema.
A lokacin wannan zagaye, al’ummar Dawakin-tofa sun kasu kashi uku. Kashin farko
sun amince da maganganun waɗannan mutane saboda tsananin ƙiyayayrsu ga PDP a ƙarƙashin
jagorancin Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan. Wasu kuma sun amince tare da amanna
da su saboda ganin girma da darajar Gwamnan Kano Rabi’u Musa Kwankwaso da
Mataimakinsa Dakta Abdullahi Ganduje.
Kashi na biyu sune wadanda kwata-kwata basu amince da maganganun waɗannan mutane ba domin sun san dama ce kawai ta suɓuce
daga hannunsu da kuma jagororinsu saboda lokacin da damar jagorancin PDP ɗin ya
ke hannunsu ai ba a ji kansu ba. Domin haka a yanzu suna so su yi amfani da
wannan dama don su yaudari mutane.
Kashi na uku sune wadanda suka tsaya a tsakiya, su basu gaskata ba, su basu
ƙaryata ba, illa dai kawai sun zuba musu ido da zummar cewa lokaci shi zai nuna
gaskiyar komai. Ga shi kuma lokacin ya fara nunawa.
Tun ba yau ba, ni ina ganin cewa mafi yawan ‘yan siyasa kusan duk halinsu ɗaya
wato son zuciya da kuma kokarin kama karya ta hanyar ƙarfa-ƙarfa da handame
dukkan wata dama. Don haka ina daga cikin wadanda suke da matuƙar shakku akan APC tun daga sama har ƙasa. Kowa ya riga ya san
ita PDP azzaluma ce gar da gar wani lokacin ma ko ɓoyewa ba ta yi, amma ita
kuwa APC munafuka ce wacce ta ke nuna adalci a fili amma zalunci a ɓoye. Ko
kuma ta yi adalci akan abu mara tasiri kamar jin ra’ayoyin mutane misali amma kuma ta yi zalunci akan abu mai
matuƙar tasiri kamar fidda ‘yan takara.
Duk da wannan tunani nawa, kullum addu’a na ke yi, Allah SWT Ya sa kada ya zama gaskiya. Allah
Ya sa APC ta bai wa wannan tunani nawa kunya ta hanyar yin gaskiya da adalci,
amma kash! Hakan ba ta samu ba.
A karamar hukuma ta ta Dawakin-tofa, Kwankwasiyya ta karɓe ragamar
jagorancin APC ta danne sauran jam’iyyu, kai ka ce ACN, CPC, ANPP su suka shigo
suka samu Kwankwasiyyar a cikin APC ba
wai Kwankasiyyar ce ta shiga ta same su ba.
Jagorancin APC a hannun Kwankwasiyya
a Dawakin-tofa ba shi ne abin damuwa ba, domin dama a siyasa mai ƙarfi, mulki,
kuɗi da jama’a ai shi ne da jagoranci. To amma kama karya mai kama da rainin
hankali da ake yi a wajen fidda ‘yan takarkarin shugabancin karamar hukuma da kansiloli
ita ce abar damuwa.
Abin sai ka ce wasan yara, wai an kafa an tsare, dole sai ‘yan Kwankwasiyya
ne za su yi takarar kansiloli ko ana sonsu ko ba a sonsu. Kuma a cikin ‘yan Kwankwasiyyar
ma sai shafaffu da mai. Wannan katoɓara ce ba ƙarama ba.
Tun farko da an san wannan tsarin za a yi, da ba sai an wahalar da mutane
ta hanyar yaudararsu cewa su fito takara dimokraɗiyya da adalci za a yi ba. Ashe
duk maganar adalci, haɗin kai, dimokradiyya, ci gaba da kyautatawa da suke yi
ashe duk yaudara suke wa mutane?
Ita kuma jam’iyyar ANPP ta Dawakin-tofa wacce za ta ɗan iya taɓuka wani abu
na gyara akan wannan lamari, ta samu kanta a ƙarƙashin jagorancin mutane marasa
kishi wadanda buƙatar kansu ce kawai a gabansu.
Idan kana takarar kansila, dole sai an sa ka ka janye ta ƙarfin tsiya ko baka
so ta hanyar baka tsoro da yi maka barazana. Idan kuma ka ƙi sai a shirya wani
haramtaccen zaɓe a kada kai. Shin kundin tsarin mulkin jam’iyyar APC ba ‘yar
tinƙe yace a yi ba ne idan sulhu bai yiwu ba?
Masu yin wannan kama karya su tuna cewa fa kafin su, dubannan mutane sun
samu wannan dama kuma yau ba ta hannun su sannan bayansu kuma damar za ta koma
hannun wasu. Su tuna kama karyar da ANPP ta yi a zaɓen kananan hukumomi na
2007, yau ina ANPP? Ta tarwatse kuma ta wulaƙanta. Itama PDP duk wannan
zaluncin da ta ke yi a Najeriya, za ta tarwatse a kan idonmu inshaAllah, domin
Allah ba Ya barin masu kama karya, sai dai ya jinkirta musu kawai. Suma ANPP ɗin
yana sonsu da shiriya shi ya sa ya koya musu hankali tun da wuri.
Na san ‘yan Kwankwasiyya suna ganin za su ci zaɓe ko ana so ko ba a so.
Wannan gaskiya ne, to amma su tuna mai zai je ya zo, ba wai yanzu ba, a’a
watarana.
Ya kamata wannan katoɓarar da APC take yi a Dawakin-tofa da sauran kananan
hukumomin Jihar Kano su daina. Idan kuma ba za su iya dainawa ba to su rage
domin aƙalla abin ya ɗan dace da hankali domin yanzu abin ya yi muni da yawa.
Allah ya kyauta.
19/11/2013
Nazari Akan Alƙiblar Siyasar Dawakin-Tofa Idan
Kwankwaso Ya Koma APC
Daga: Amir Abdulazeez
Siyasa mai abin mamaki da kuma abin
dariya. A siyasa ne, sai ka gama kushe mutum ciki da bayansa saboda bambancin
ra’ayi sai kuma ku wayi gari a jam’iyya ɗaya kuma akan manufa ɗaya tare kuma da
neman makoma iri ɗaya. Wani lokacin kuma sai ka gama yin Allah wadai da wata
jam’iyya, sai ka samu kanka tsamo-tsamo a cikinta.
Idan banda haka, da Janaral Muhammadu
Buhari ba za su zauna jam’iyya ɗaya da Cif Bisi Akande, shugaban riƙo na APC na
ƙasa ba domin kuwa lokacin da Buhari ya yi juyin mulki, Bisi Akande shine
Mataimakin Gwamna Bola Ige na Jihar Oyo kuma Buhari ya yanke musu ɗaurin
shekaru barkatai a kurkuku dukkansu su biyun, amma yanzu gasu nan ba mai jin
kansu. Yau ga Mallam Nuhu Ribadu a teburi ɗaya da mafi yawan mutanen da ya kira
ɓarayi kuma maciya amana lakoacin da yake shugaban hukumar EFCC. Gashi yau babu
amintattu masu gaskiya a gunsa kamarsu saboda jam’iyyarsu ɗaya..
Anan Kano ga Mallam Ibrahim Shekarau ya
sake haɗewa da tsofaffin mataimakansa, Injiniya Magaji Abdullahi da kuma
Injiniya Abdullahi Tijjani Gwarzo waɗanda suka rabu baran-baran, kuma mai
yiwuwa nan da wasu ‘yan kwananki zai haɗe da babban kishiyarsa wato Dakta
Rabi’u Musa Kwankwaso a cikin tafiya guda.
Dukkan alamu tun daga sama har ƙasa sun
nuna cewa, Gwamna Rabi’u Musa Kwankwaso yana kan hanyarsa ta shigowa jam’iyyar
APC. Koda yake ba za mu iya tantacewar ko za su shigo ne gabaɗaya tare da
sauran ‘yan uwansa gwamnoni waɗanka aka fi sani da ‘yan 7 ko G-7, ko kuma shi
kaɗai zai shigo ba. Amma babu shakka shigowarsa APC a yanzu zai canja al’amuran
siyasa a Jihar Kano, wataƙila ma har da Najeriya baki ɗaya.
Anan Dawakin-Tofa, wani babban jigo a
jam’iyyar PDP wanda bai bamu izinin bayyana sunansa ba ya tabbatar mana da cewa
jam’iyyar tana kiran taro a kowacce mazaɓa don jin ra’ayin ‘ya’yanta, kuma kawo
yanzu dukkan mazaɓun da suka ziyarta sun jaddada goyon bayansu ga Maigirma
Gwamna kuma umarninsa kawai suke jira. Duk da cewa bai bayyana mana mazaɓun da
aka gudanar da wannan taro ba, amma Muryar
Dawakin-Tofa ta halarci taron da aka gudanar a mazaɓun Dawanau da Ƙwa, kuma
tana sane da lokacin da aka gudanar da taron a mazaɓar Tumfafi, bugu da ƙari
kuma ta san lokacin da ake shirye-shiryen gudanar da wannan taro a mazaɓun
Dawakin-Tofa ta Gabas da Dawakin-Tofa ta Yamma.
To, ko ma dai da irin wannan taruka ko
babu, dukkan mai bibiya ko nazari akan al’amuran siyasar PDP Kwankwasiyya, ya
san cewa tafiya ce da aka gina ta akan umarni da kuma biyayya, wannan ce ma ta
sa mutane da yawa za su yi mamakin yin taron jin ra’ayin jama’a saɓanin yadda
aka saba a baya na a yanke hukunci sannan a turo umarni daga sama zuwa ƙasa.
Wannan ya nuna jan ƙafa da kuma ɗar-ɗar ɗin da shi kansa Gwamna Kwankwaso yake
yi kafin shigarsa APC ɗin.
Duk da cewa akwai tsirarun ‘yan
Kwankwasiyya anan Jihar Kano da ake sa ran ba lallai su bi Kwankwaso zuwa APC
ba, to amma da wahala a samu irinsu a nan Dawakin-Tofa. Koda yake a ‘yan
kwanakinnan raɗe-raɗe sun cika gari cewa Mataimakin Gwamna, Dakta Abdullahi
Umar Ganduje ba zai bi Kwankwaso izuwa wata sabuwar jam’iyya ba, amma kuma
makusantansa sun fito sun ƙaryata wannan jita-jitar ta hanyar sanarwa a kafafen
yaɗa labarai cewa Ganduje yana tare da Kwankwaso ɗari bisa ɗari komai ruwa komai
iska.
Shi kansa Sakataren Yaɗa Labaran
Ofishin Mataimakin Gwamnan, Bala Salihu Dawakin-Kudu da muka tuntuɓe shi, ya yi
watsi da jita-jitar a matsayin aikin ‘yan adawa.To tunda ‘yan PDP Kwankwasiyya
na Dawakin-Tofa, babu wanda suka sani banda Ganduje, to da wahala wani ya
bijire.
Wani bincike da muka gudanar, ya nuna
cewa, wasu daga cikin ‘yan Kwankwasiyya a Dawakin-Tofa za su bi Kwankwaso izuwa
APC ne saboda basu da wani zaɓi amma ba don suna so ba saboda sun riga sun ɓata
da kowa, kuma sun yi watsi da duk wani ɗan siyasa sun riƙe Kwankwaso da
Ganduje. Don haka basu da kowa sai su, to kuma yanzu an kawo gaɓar da ba za su
iya sauya iyayen gida ba. Wasu kuma za su bi ne saboda suna morar gwamnatin
kuma ba za su so su rabu da mulkin ba.
Wani babban jigo a PDP wanda sha’anin
komawarsa APC yake da ‘yar sarƙaƙiya da kuma rikitarwa shine Ɗan Majalisar
Dokokin Jihar Kano Mai Wakiltar Ƙaramar Hukumar Dawakin-Tofa, Honarabul Saleh
Ahmed Marke domin shi akwai tanadin doka a cikin tsarin mulkin Najeriya wacce
ta tanadi cewa duk wani ɗan majalisa ba zai iya sauya jam’iyya ba sai ya yi
asarar kujerarsa, koda yake zai iya fakewa da cewa ai jam’iyyar tasa ta rabe
gida biyu. Amma idan aka yi la’akari da ƙarfin nufi da kuma zafin kishi irin na
ɓangaren tsohuwar PDP ƙarkashin Alhaji Bamanga Tukur wacce ta yi barazanar
tabbatar da cewa dukkan wani ɗan majalisa ɗan sabuwar PDP da ya bar PDP, to ya
rasa kujerarsa. Kuma dolene a ɗauki wannan barazana da matuƙar muhimmanci, duba
da cewa shugaban ƙasa a ɓangarensu yake banda kuma kotuna da lauyoyi da suke
dasu.
Idan muka kalli jiga-jigan da suke
cikin PDP da waɗanda suke cikin APC a Dawakin-Tofa, sai mu tambayi kanmu: wai
shin idan suka cakuɗe waje guda, siyasar ma zata yiwu kuwa? Gashi dama dukkan
manyan Dawakin-Tofa basa wuce wannan jam’iyyun guda biyu tun daga 1999. Ko
shakka babu girma da muhimmancin wasu dole ya ragu saboda tsananin gasa da
takara da za’a samu. Wata tambayar ita ce: shin za’a samu sauran wata jam’iyyar
adawa kuwa? Babu mamaki ƙanana da sababbin jam’iyyu irinsu PDM da LABOUR PARTY
su yi amfani da wannan dama su kawo kansu Dawakin-Tofa kuma mai yiwuwa su samu
tarin magoya baya. Bayan haka, kada a manta da cewa akwai ‘yan tsohuwar PDP a
Dawakin-Tofa waɗanda ba ‘yan Kwankwasiyya ba kuma suna nan za su yi zamansu daram
a PDP tare da samun isasshiyar iskar shaƙa da sararin watayawa. Banda haka, za
su samu dukkan goyon baya da gudunmawar da suke buƙata tun daga Abuja har zuwa
kan Hassan Kafayos banda kuma Biloniya Muhammad Abacha wanda a shirye yake ya
taimakesu. Duk da cewa ba’a san wanda zai jagoranci waɗannan mutane ba, to amma
akwai Dakta Mahmood Baffa Yola, Babban Kwamishina a Jihar Kano na Hukumar
Karɓar Ƙorafe-Ƙorafen Jama’a ta Tarayya. To amma wani hanzari ba gudu ba shine,
kowa ya san kusancin Dakta Mahmood da Sanata Bello Hayatu Gwarzo wanda ana
ganin duk inda za su a siyasance, tare za su je. Shi Maigirma Sanata, a farkon
wannan rigima, an rawaito shi a cikin sanatoci 22 na sabuwar PDP amma kuma
yanzu alamu sun nuna ya yi baya-baya duk da cewa yana da kyakkyawar alaƙa da
Kwankwaso tun ba yau ba. Don haka ba za’a iya sanin inda Dakta Mahmood ya nufa
ba sai an tantance makomar Sanata. To amma wani abin dubawa anan shine, idan
har ‘yan tsohuwar PDP suka samu Dakta Mahmood Baffa Yola a matsayin jagora, to
akwai yiwuwar su yi babban tasiri kasancewar mutane da yawa na yi masa kallon
dattijon arziki wanda yake iya riƙe mutane.
Yanzu haka kuma guna-guni ya yawaita a
cikin ‘yan APC ɗin da basa maraba da shigowar Gwamna Kwankwaso da Ganduje
cewar, a ranar da suka shigo APC, su kuma kashegari za su sauya sheƙa zuwa PDP.
Ko wannan barazana tasu gaske ce ko kuma kuri ce? Lokaci shi zai yi alƙalanci.
Rahotanni sun nuna cewa su ‘yan tsohuwar PDP waɗanda aka yiwa laƙabi da ‘yan
Garkuwa har sun fara shirye-shiryen kafa shugabancin riƙo na jam’iyyar a nan
Dawakin-Tofa, wasu ma sun tabbatar da cewa an kafa wannan shugabanci ta
ƙarƙashin kasa.
Ita kanta sabuwar amaryar wato APC,
masana suna ganinta da tarin matsaloli iri-iri anan Dawakin-Tofa. A bayyane
yake a fili cewa ‘yan tsohuwar ANPP sun riga sun kankane jam’iyyar tun kafin a
je ko’ina kuma a shirye suke da su kafa shugabancinta ko da kuwa babu haɗin kan
CPC da ACN. Abinda kawai zai hanasu cimma burinsu shine Injiniya Magaji
Abdullahi wanda shine turken CPC. To amma idan aka yi la’akari da cewa kusan
dukkan mutanen CPC da ANPP ɗin duk mabiyansa ne na da da na yanzu, ba lallai ne
ya damu da waɗanda za su zama shugabanni ba. Ita kanta tsohuwar CPC ɗin ta
Dawakin-Tofa, wani tsagi nata ana kyautata zaton ya bi Sanata Rufa’i Sani Hanga
zuwa Jam’iyyar PDM. Rigimar da ta fatattaka ANPP zuwa CPC da ACN babu tabbacin
ta warware, me yiwuwa ta ciki na ciki. To amma idan aka yi la’akari da aiki ba
dare ba rana da wata ƙungiya mai rajin tabbatar da adalci da dimokraɗiyya a APC
take yi, sai mu iya cewa za’a samu gyara. Wannan ƙungiya ta haɗa jiga-jigan
tsofaffin ANPP, CPC da ACN ɗin. To amma matsalar shine, har yanzu da alamun
cewa jiga-jigan tsohuwar ANPP basu yi amanna da wannan ƙungiya ba.
Wannan shine halin da APC take a yanzu,
to yaya kuma a ce PDP Kwankwasiyya ta antayo cikinta?
Wani mutum da zai iya yin gagurumin
tasiri a wannan rintsi shine, Ɗan Majalisar Tarayya Mai Wakiltar Dawakin-Tofa,
Tofa da Rimin-Gado, Honarabul Tijjani Abdulkadir Joɓe domin kuwa ko ba komai a
shekaru shida da ya shafe akan mulki, ya kafa sansani mai ƙarfi nasa na kansa
anan Dawakin-Tofa wanda tunɓuke shi ko hanashi tasiri zai yi wahala. Kuma a
matsayinsa na wanda yake riƙe da mulki, ko da ‘yan Kwankwasiyya sun shigo ba
dolene su yi masa wani mummunan rauni ba musamman idan bai nuna zai yaƙesu
ba.
A yanzu bata fito fili akan wanene yake
jagorantar jam’iyyar APC a Dawakin-Tofa ba tsakanin Injiniya Magaji Abdullahi
da Dakta Maikano Rabi’u ba, balle kuma a ce ga Dakta Ganduje ya shigo. Gefe
ɗaya kuma akwai jiga-jigai irinsu Mallam Alhassan Dawaki, Honarabul Saleh Shehu
Kwuidawa da sauransu waɗanda har yanzu ba’a ji ƙwaƙƙwaran motsinsu ba. Ko kuma
dan ba’a buga gangar siyasar ba ne?
A ƙarshe dole mu bar wa lokaci damarsa
domin shi ne zai warware mana dukkan wannan ƙulle-ƙulle amma babu shakka za mu
sha kallo nan ba da daɗewa ba domin kuwa koda Kwankwaso bai shigo APC ba to
akwai yiwuwar ya bar PDP.
Matsalolin Ƙaramar
Hukumar Dawakin-Tofa: Surutu Ba Zai Kaimu Ko’ina Ba
7th November, 2013
Daga:
Amir Abdulazeez
(08032202869,
abdulazeezamir@hotmail.com)
“Na duba dukkan abokai amma ban samu abokin da ya fi kiyaye harshe ba.”
- Umar Ibn Al-Khattab (RA)
N
|
i a ganina, surutu iri uku ne; akwai surutu mai ma’ana
kuma mai amfani, akwai surutu mai ma’ana amma mara amfani sannan akwai surutu
mara ma’ana kuma mara amfani. Kowanne ɗaya daga cikin waɗannan nau’ika na
surutu, akwai yanayi da muhallin da suka dace da shi.
Surutu mai ma’ana kuma mai amfani shine mutum ya yi magana
akan abin da ya dace kuma a inda ya dace ko da kuwa zai kwana yana magana.
Misali, idan za ka yi magana akan matsalar ilimi a ƙaramar hukumar Dawakin-Tofa,
to ka tabbatar cewa kai masanin ilimi ne, in kuma ba haka ba, to ka tabbatar ka
yi bincike kuma ka fahimci abin da ka ke magana akansa. Bayan haka sai ka nufi
gurin waɗanda abin ya shafa kamar ofishin ma’aikatar ilimi misali sai ka baje
kolinka a can. Ka ga anan kowa ya san surutunka na a kawo gyara ne.
Surutu mai ma’ana amma kuma mara amfani shine mutum ya yi
magana akan abin da ya dace amma ba a inda ya dace ba. Misali shine, za ka yi magana
akan matsalolin asibitin Dawakin-Tofa, sai aka yi sa’a ka yi cikakken bincike
ka san matsalolin asibitin ciki da bai kuma kana da isassun hujjoji amma kuma
sai aka wayi gari ka je gaban teburin mai shayi kana baje kolinka. To anan kaima
da kanka, ka san ba gyara kake nema ba.
Shi kuwa surutu mara ma’ana kuma mara amfani bai kamata
ma ya samu muhalli a gurin da aka san ciwon kai ba. Domin kuwa shine surutun da
mutum zai dinga yin magana akan abin da bai sani ba ko bai fahimta ba kuma ya ƙi
ya yi bincike akaisannan kuma ya dinga yin wannan surutun a gurin da bai dace
ba. Idan da ma zai yi shi a gurin da ya dace, da sai a samu masu yi masa gyara
ko tsokaci. Wani lokaci kuma mai irin wannan surutan, idan ka yi masa gyara to
sai cibi ya zama ƙari. Irin waɗannan surutan ne wasu daga cikinmu suke yi a
majalisu, guraren hira da kuma dandalin sada zumunta na facebook da sauran waɗansu kafafe. Wataƙila suna sane, ƙila kuma
basu sani ba.
Shi dai surutu ko da akan alkhairi ne, idan ya yi yawa to
ya kan zama illa ba ƙarama ba ga mai yinsa, balle kuma a ce akan sharri ake
yawan yinsa.
Sanin kowa ne cewa mun wayi gari a ƙaramar hukumar
Dawakin-Tofa, babu abin da muke yi sai kushe ƙaramar hukumarmu, ba babba ba
yaro. Abin haushinma shine har da waɗanda basu ma cancanta su ce uffan ba idan
ana maganar ƙaramar hukumar domin kuwa babu wata gudunmawa da suka taɓa bata,
suma sun samu dama har kusheta suke yi. Bayan haka kuma gamu da kushe masu riƙe
da madafan iko, na da da na yanzu da kuma sauran manyan mutane. To ba laifi don
ka faɗakar da wanda yake da dama a hannunsa kuma bai yi amfani da ita ba don
kawo cigaba, amma kafin ka yi hakan sai ka yi tunanin kaima damar da take
hannunka komai ƙanƙartarta, amfanin me ka yi da ita domin cigaban ƙaramar
hukumarka? Kuɗi da mulki ba sune kaɗai dama ba, lafiya, lokaci, ilimi, sana’a
duk suma damammaki ne.
Ni na san cewa Dawakin-Tofa ta samu cigaba ta fannoni da
yawa amma ba ma gani. Idan muka ɗauki misali a ɓangaren ilimi; kafin shekarar
2003, na san garuruwa da ƙauyuka da yawa a ƙaramar hukumar Dawakin-Tofa waɗanda
basu da ko mutum ɗaya wanda ya gama makarantar gaba da sakandire walau a
matakin Digiri, Diploma ko NCE. Ba zan faɗi sunan garuruwan ba amma a yanzu da
wahala ka samu garin da za’a ce babu mai Digiri, Diploma ko NCE ko mutum ɗaya
komai ƙauyancin garin. Wannan cigaba ne kuma dama shi cigaba ai da sikeli ake
amfani ba wai da surutu ba. Aunawa ake yi a ga me kake da shi da kuma me kake
da shi yanzu?
Na sani cewa, akwai ƙananan hukumomi da yawa da suka sha
gabanmu a wasu fannoni na rayuwa amma mu ma mun sha gaban wasu ƙananan hukumomin
a wasu fannonin. Misali, idan kace Bichi ta sha gabanmu ta fuskar ilimin boko,
to ƙila mu kuma mun sha gabansu ta fuskar Ilimin Addini ko kuma ta fuskar noma.
Idan kuma burin wannan surutai namu shine mu wayi gari
mun sha gaban kowacce ƙaramar hukuma a Jihar Kano ta kowanne fanni na rayuwa,
to abin mai sauƙi ne, ba na tashin hankali ba ne. Abin da za mu yi shine,
wannan buhunnan surutan namu, mu zazzage su mu ɗure su da aiki tuƙuru. Mu daina
nunawa kowa yatsa, mu bazama, kowa a fanninsa ya dage ya ga ya kawo wani cigaba
a karan kansa. Ya yi ta aiki ba ƙaƙƙautawa, inda ya gaji ko ya tsaya ko ya
kasa, to sai wani ya ɗora har sai mun cimma burinmu.
Idan kuma muna ganin ba zamu iya haƙura da surutun ba, to
ga wata shawara. Mu zaɓi wasu ɗaiɗaiku daga cikinmu mu ɗora musu alhakin shirya
mana taron tattaunawa ko muhawara duk wata ko duk bayan wata uku a dinga zama a
mazaɓa ɗaya ko a mazaɓu daban-daban, kowa yana faɗar albarkacin bakinsa kamar
yadda aka yi a taron farfado da ilimi a kwanakin baya. Duk da dai cewa har
yanzu taron farfaɗo da ilimin bai fara kawo wani sakamako a aikace ba amma ko
ba komai an yi muhawara a ranar taron. Amma idan za’a yi irin wannan taro, sai
a yi abin a natse kuma a hankalce tare da tattauna yadda za’a shawo kan
matsalolinmu a aikace maimakon soki burutsu. Amma idan ba haka ba to irin
wannan surutun ba zai kaimu ko’ina ba.
No comments:
Post a Comment