24 GaOktoba, 2013.
Daga:
Amir Abdulazeez
alilai biyu ne suka sa ni yin rubutu akan wannan batu duk da cewa akwai
dubunnai irina da suka sha yin sharhi da rubuce-rubuce akan cin hanci da
rashawa a Najeriya.
Dalili na farko, a shekarar 2009 na kai wa wani aminina
ziyara, mu na zaune mu na tattaunawa sai wani matashi wanda nake tsammanin su
na da wata alaƙa da shi ya zo inda mu ke. Daga ganin alamarsa a buge ya ke ko
kuma ya na yawan buguwa da kayan maye. Wannan matashi sai ya tambayi amininnan
nawa N500 akan zai yi kuɗin mota zuwa ƙauyensu
saboda ya karɓo takardar shaidar zama ɗan asalin ƙaramar hukumarsu domin ana
dab da ɗaukarsa aikin ɗan sanda kuma lallai ne za’a buƙaci wannan takarda.
Wannan aminin nawa sai ya ɗauko N 500
ya bashi, sai ya tafi. Bayan ya tafi sai ya juyo ya kalleni, yace: ‘abokina, Najeriya
ba za ta taɓa gyaruwa ba’. Na tambayeshi, me ya sa? Sai yace: ‘ka duba wai
wannan bugaggen, mara tarbiyyar za’a ɗauka aiki mai muhimmanci irin na ɗan
sanda wanda kuma in da rai da rabo, watarana shi ka ke sa ran zai zama shugaban
‘yan sandan Najeriya. Na girgiza kai, ban sake cewa komai ba amma na kai tsawon
shekaru huɗu ina jinjina wannan magana ta sa, sai yanzu na samu cikakken ilimi
da kuma kafar da zan yi tsokaci akan abin da ya gaya min.
Amma kafin in kawo dalilina na biyu, ga wasu tambayoyi.
Shin me zai sa Dagatai da Masu Unguwanninmu su dinga sanyawa mutane hannu akan
takardar shaidar zama ɗan asalin yankinsu ba tare da sun tantance amfanin da
mutum zai yi da takardar ba? Me zai sa ba za su yi ƙoƙarin hana mutane irin waɗannan
shiga irin wannan aiki ba ta hanyar bada mummunar shaida akansu? Ko kuwa ba su
da wani zaɓi, tunda mutanen kirki duk sun guji aikin sai mutanen banza ne da
kuma waɗanda suka rasa aikin yi su ke shiga aikin? To ko shi ya sa rundunar
sojoji, ‘yan sanda da sauran masu ɗamara ta Najeriya ta cika da ma su karɓar cin hanci da rashawa?
Dalilina na biyu na yin wannan rubutu shi ne; an taɓa
gayyata ta wani taro da wata ƙungiya mai fafutukar yaƙi da cin hanci da rashawa
anan Jihar Kano ta shirya a shekarar 2011 a Ɗakin Karatu na Jihar Kano. Taken
wannan taro shi ne: ‘Gudunmawar da zan
Bayar a Matsayina na ɗan Ƙasa Wajen Kawar da Cin Hanci da Rashin Gaskiya a Najeriya’.
Wannan taro ya samu halartar ƙwararru da dama, ciki har da wakilan hukumar yaƙi
da cin hanci ta ICPC. Duk da cewa taken wannan taro ya bayyana mana ƙarara cewa
ana so ne kowa ya faɗi me ya ke ganin ‘yan Najeriya za su yi a matsayinsu na waɗanda
ake mulka domin kawar da cin hanci da cin amana a ƙasarnan, amma abin takaici, mahalarta
wannan taro, waɗanda kuma aka kira da ƙwararru, duk wanda ya miƙe maimakon ya
yi magana akan abin da aka tsara sai ya ɓige da zagin Shugaban Ƙasa, ‘yan
majalisu, ministoci, ‘yan siyasa da sauran ma su mulki. Ni kaɗai na fita zakka,
yayin da aka bani damar magana sai na tunatar da mahalarta taron cewa ya kamata
mu daina barin jaki muna dukan taiki, kamata ya yi mu kalli namu matsalolin
kafin mu kalli na shugabanninmu. Kafin kace kwabo, sai aka yi min caa a ka, wai
ai babu laifin mabiya, ai shugabanni ne ɓarayi don haka dole a faɗa, kai a taƙaice
ma ni ban san me na ke yi ba. Ganin cewa babu wanda ya goyi bayana, sai na
sulale cikin kunya na fita daga wannan taro kuma ban ƙara waiwayar wannan magana
ba sai yanzu.
Abin tambaya anan shine, wai me ya sa sau dubu sai mu
take laifin mu amma muna da idon hango na shugabanninmu? Wai me ya sa, sai
mutum ya tafka ta’asar da ya ga dama, idan an yi magana wai sai yace ai haka Najeriya
ta ke, kowa ba shi da gaskiya don haka ma in ka yi gaskiya kana ɓatawa kanka
lokaci ne kawai? Wai me ya sa dukkan abin alkhairin da ƙasarmu ta yi, ba ma faɗa
amma komai ƙanƙantar sharri ko da ba mu yi bincike mun tabbatar da shi ba sai
mu yi ta yayata shi? Shin wai lalacewar Najeriya ya kai yadda mu ke kururutawa
kuwa? Wai muna kallon wasu ƙasashen na ƙasa da mu ko kuwa muna la’akari ne
kawai da na sama da
mu?
Tunda munji waɗannan dalilai, bari na dawo kan tambayata
ta asali, shin wanene zai kawar da cin hanci da rashawa a Najeriya? Wannan tambaya
tana da wahalar amsawa kai tsaye kuma tana da amsoshi da yawa domin kowa a Najeriya
idan ka tambayeshi, yana da amsar da zai bayar akanta. Amma kafin na bayar da
tawa amsar ina so mu sani cewa, kowa da kowa ya na da gudunmawar da zai bayar
wajen gyaruwar Najeriya ko lalacewarta komai girmansa kuma komai ƙanƙantarsa.
Babu wani shugaba a duniya komai nagartarsa da zai iya
zuwa ya ci nasarar kawo wani gyara ko canji a rayuwar mutane ba tare da su
mutanen sun ba shi haɗin kai ba. Wannan shi ya tuna min da wani furuci na
tsohon Shugaban Ƙasa Cif Olusegun Obasanjo inda ya ke cewa: “Dole ne idan za ka yi maganar kyakkyawan
shugabanci, to ka yi maganar ingantattun mabiya.” Bayan wannan, za mu iya ɗaukar
darasi daga gurin Joseph Stalin na tsohuwar rugujajjiyar Tarayyar Soviet wacce
ita ce ƙasar Russia a yanzu wanda ya mulki tarayyar na tsawon kusan shekaru 25.
Ya yi sanadiyyar mutuwar tsakanin mutane miliyan 5 zuwa 10 a ƙudurinsa na kawo
wasu sauye-sauye a ƙasar, amma duk da haka bai cimma nasara cikakkiya ba domin
ya na
mutuwa sauye-sauyen na
sa suka ruguje domin mutane ba sa tare da su.
Anan, ko kusa ba ni da niyyar in tsame shugabannin Najeriya
daga laifukan da ake zarginsu da shi
domin na yarda cewa sun a da laifuka ma su yawan gaske, amma ya
kamata mu sani cewa waɗannan shugabannin ba aljanu ko mala’iku ba ne, ko kuma
ba sauko mana su aka yi daga sama ba, daga cikinmu suke fitowa. Don haka ashe
mu ɗin ne a lalace kenan? Wani abin lura da shi anan shi ne, mun sha juyawa
shugabanninnan baya a zaɓe ta hanyar musanyasu da wasu kuma ƙarshe su ma waɗanda
mu ka sauya ɗin su ba mu kunya. To tunda shugabanninan daga cikinmu su ke
fitowa, wajibi ne sai mun gyara kanmu.
Bugu da ƙari, duk irin satar kuɗin jama’a da
shugabanninmu suke yi, mu talakawa
mu mu ka ba
su dama. A yanzu da mutum zai riƙe muƙamin Gwamna ko shugaban ƙaramar hukuma
kuma ya sauka ba
shi da naira miliyan 100 misali ko kuma ya sauka ya cigaba da rayuwar da ya
saba da ita kafin yan
hau muƙamin, sai ka ji ana zaginsa ana cewa ba shi da ƙashin
arziki. Ko muna tsammanin ma
su riƙe da muƙaman ba su san
wannan ba? Mu tuna fa cewa, idan zaɓe ya zo, masu mulki ne da masu neman mulki
suke zagayawa su
na raba mana cin hanci don mu zaɓe su. Wasu daga cikinmu ma har yawo suke
yi da ganye a ka, wai su
na sayarwa ne.
Wai meye cin hanci ne? Cin hanci shi ne duk wani
abu da za’a ba
ka na kuɗi ko na amfani wanda zai sa ka ka
yi abin da
ba shi
ya kamata a yi ba a wannan muhallin.
Mu ɗinnan ne fa mu ke taruwa a gidaje da ofisoshin masu
mulki mu na tilasta
mu su
su bamu kuɗi duk da cewa mun san cewa albashinsu bai kai su bamu
abinda mu ke nema a gurinsu
ba. To tsammaninmu a waɗanne kuɗaɗen su ke ɗebowa su na bamu?
A cikin wannan al’aumma tamu ne, ba’a ganin mutunci ko
darajar mutum akan iliminsa, gaskiyarsa ko iya mu’amalarsa, sai dai akan kuɗinsa
kuma ba tare da anyi duba da hanyar da ya bi ya samu waɗannan kuɗin ba.
Mu tuna fa mutum ne zai saci kuɗin mutane, amma sai ka ga ya fito ana
kwanciya ana gaida shi. A nan garin ne wani ya yi zaman kurkuku na kusan
shekaru biyu saboda kotu ta yanke masa hukuncin cewa ya saci kuɗin jama’a. Amma ranar da ya
fito, sai da talakawa suka
yi gangamin taron
tarbarsa da kuma girmamashi. To anan wanene ya ke ɗaurewa
cin hanci gindi, mu ne ko kuwa shugabanninmu?
Don haka ko shakka babu, amsata ita ce, mu
talakawa mu muke da kaso mafi tsoka wajen hana cin hanci da rashawa a Najeriya
duk da cewa su
ma shugabannin akwai rawar da za
su taka ba ƙarama ba.
Duk mai tunanin gyara a Najeriya, ya fara kallon kansa tsaf, ya ga shi a gyare
ya ke? Mutum ya gyara
kansa, ya yi gaskiya akan kansa, sannan sai ya yi ƙoƙarin gyara gidansa. Idan ya gama da gidansa, sai ya fara
tunanin gyaran unguwarsu, sannan ƙaramar hukumarsu, sannan jiharsa, kafin ya
fara tunanin Najeriya.
Cin hanci da rashawa
da sata ba za su taɓa rabuwa da mu ba, sai mun yi gaskiya a
kasuwancinmu, aikinmu, iyalinmu, ƙungiyoyinmu, abotarmu, Masarautunmu da dukkan
al’amuranmu.
Bayan mun yi wannan, sai
mu kalli
shugabanninmu ido da ido, mu ci kwalar rigarsu,
ƙila ma har da lakace mu su hanci sannan mu ce mu su: me ya sa ba ku da gaskiya?
©2013: abdulazeezamir@hotmail.com