Translate

Monday, January 20, 2014

Wa Zai Kauda Cin Hanci da Rashawa a Najeriya?

24 GaOktoba, 2013.

Daga: Amir Abdulazeez
                                                                                         
D

alilai biyu ne suka sa ni yin rubutu akan wannan batu duk da cewa akwai dubunnai irina da suka sha yin sharhi da rubuce-rubuce akan cin hanci da rashawa a Najeriya.
Dalili na farko, a shekarar 2009 na kai wa wani aminina ziyara, mu na zaune mu na tattaunawa sai wani matashi wanda nake tsammanin su na da wata alaƙa da shi ya zo inda mu ke. Daga ganin alamarsa a buge ya ke ko kuma ya na yawan buguwa da kayan maye. Wannan matashi sai ya tambayi amininnan nawa N500 akan zai yi kuɗin mota zuwa ƙauyensu saboda ya karɓo takardar shaidar zama ɗan asalin ƙaramar hukumarsu domin ana dab da ɗaukarsa aikin ɗan sanda kuma lallai ne za’a buƙaci wannan takarda. Wannan aminin nawa sai ya ɗauko N 500 ya bashi, sai ya tafi. Bayan ya tafi sai ya juyo ya kalleni, yace: ‘abokina, Najeriya ba za ta taɓa gyaruwa ba’. Na tambayeshi, me ya sa? Sai yace: ‘ka duba wai wannan bugaggen, mara tarbiyyar za’a ɗauka aiki mai muhimmanci irin na ɗan sanda wanda kuma in da rai da rabo, watarana shi ka ke sa ran zai zama shugaban ‘yan sandan Najeriya. Na girgiza kai, ban sake cewa komai ba amma na kai tsawon shekaru huɗu ina jinjina wannan magana ta sa, sai yanzu na samu cikakken ilimi da kuma kafar da zan yi tsokaci akan abin da ya gaya min.

Amma kafin in kawo dalilina na biyu, ga wasu tambayoyi. Shin me zai sa Dagatai da Masu Unguwanninmu su dinga sanyawa mutane hannu akan takardar shaidar zama ɗan asalin yankinsu ba tare da sun tantance amfanin da mutum zai yi da takardar ba? Me zai sa ba za su yi ƙoƙarin hana mutane irin waɗannan shiga irin wannan aiki ba ta hanyar bada mummunar shaida akansu? Ko kuwa ba su da wani zaɓi, tunda mutanen kirki duk sun guji aikin sai mutanen banza ne da kuma waɗanda suka rasa aikin yi su ke shiga aikin? To ko shi ya sa rundunar sojoji, ‘yan sanda da sauran masu ɗamara ta Najeriya ta cika da ma su  karɓar cin hanci da rashawa?

Dalilina na biyu na yin wannan rubutu shi ne; an taɓa gayyata ta wani taro da wata ƙungiya mai fafutukar yaƙi da cin hanci da rashawa anan Jihar Kano ta shirya a shekarar 2011 a Ɗakin Karatu na Jihar Kano. Taken wannan taro shi ne: ‘Gudunmawar da zan Bayar a Matsayina na ɗan Ƙasa Wajen Kawar da Cin Hanci da Rashin Gaskiya a Najeriya’. Wannan taro ya samu halartar ƙwararru da dama, ciki har da wakilan hukumar yaƙi da cin hanci ta ICPC. Duk da cewa taken wannan taro ya bayyana mana ƙarara cewa ana so ne kowa ya faɗi me ya ke ganin ‘yan Najeriya za su yi a matsayinsu na waɗanda ake mulka domin kawar da cin hanci da cin amana a ƙasarnan, amma abin takaici, mahalarta wannan taro, waɗanda kuma aka kira da ƙwararru, duk wanda ya miƙe maimakon ya yi magana akan abin da aka tsara sai ya ɓige da zagin Shugaban Ƙasa, ‘yan majalisu, ministoci, ‘yan siyasa da sauran ma su mulki. Ni kaɗai na fita zakka, yayin da aka bani damar magana sai na tunatar da mahalarta taron cewa ya kamata mu daina barin jaki muna dukan taiki, kamata ya yi mu kalli namu matsalolin kafin mu kalli na shugabanninmu. Kafin kace kwabo, sai aka yi min caa a ka, wai ai babu laifin mabiya, ai shugabanni ne ɓarayi don haka dole a faɗa, kai a taƙaice ma ni ban san me na ke yi ba. Ganin cewa babu wanda ya goyi bayana, sai na sulale cikin kunya na fita daga wannan taro kuma ban ƙara waiwayar wannan magana ba sai yanzu.

Abin tambaya anan shine, wai me ya sa sau dubu sai mu take laifin mu amma muna da idon hango na shugabanninmu? Wai me ya sa, sai mutum ya tafka ta’asar da ya ga dama, idan an yi magana wai sai yace ai haka Najeriya ta ke, kowa ba shi da gaskiya don haka ma in ka yi gaskiya kana ɓatawa kanka lokaci ne kawai? Wai me ya sa dukkan abin alkhairin da ƙasarmu ta yi, ba ma faɗa amma komai ƙanƙantar sharri ko da ba mu yi bincike mun tabbatar da shi ba sai mu yi ta yayata shi? Shin wai lalacewar Najeriya ya kai yadda mu ke kururutawa kuwa? Wai muna kallon wasu ƙasashen na ƙasa da mu ko kuwa muna la’akari ne kawai da na sama da mu?

Tunda munji waɗannan dalilai, bari na dawo kan tambayata ta asali, shin wanene zai kawar da cin hanci da rashawa a Najeriya? Wannan tambaya tana da wahalar amsawa kai tsaye kuma tana da amsoshi da yawa domin kowa a Najeriya idan ka tambayeshi, yana da amsar da zai bayar akanta. Amma kafin na bayar da tawa amsar ina so mu sani cewa, kowa da kowa ya na da gudunmawar da zai bayar wajen gyaruwar Najeriya ko lalacewarta komai girmansa kuma komai ƙanƙantarsa.

Babu wani shugaba a duniya komai nagartarsa da zai iya zuwa ya ci nasarar kawo wani gyara ko canji a rayuwar mutane ba tare da su mutanen sun ba shi haɗin kai ba. Wannan shi ya tuna min da wani furuci na tsohon Shugaban Ƙasa Cif Olusegun Obasanjo inda ya ke cewa: “Dole ne idan za ka yi maganar kyakkyawan shugabanci, to ka yi maganar ingantattun mabiya.” Bayan wannan, za mu iya ɗaukar darasi daga gurin Joseph Stalin na tsohuwar rugujajjiyar Tarayyar Soviet wacce ita ce ƙasar Russia a yanzu wanda ya mulki tarayyar na tsawon kusan shekaru 25. Ya yi sanadiyyar mutuwar tsakanin mutane miliyan 5 zuwa 10 a ƙudurinsa na kawo wasu sauye-sauye a ƙasar, amma duk da haka bai cimma nasara cikakkiya ba domin ya na mutuwa sauye-sauyen na sa suka ruguje domin mutane ba sa tare da su.

Anan, ko kusa ba ni da niyyar in tsame shugabannin Najeriya daga laifukan da ake zarginsu da shi domin na yarda cewa sun a da laifuka ma su yawan gaske, amma ya kamata mu sani cewa waɗannan shugabannin ba aljanu ko mala’iku ba ne, ko kuma ba sauko mana su aka yi daga sama ba, daga cikinmu suke fitowa. Don haka ashe mu ɗin ne a lalace kenan? Wani abin lura da shi anan shi ne, mun sha juyawa shugabanninnan baya a zaɓe ta hanyar musanyasu da wasu kuma ƙarshe su ma waɗanda mu ka sauya ɗin su ba mu kunya. To tunda shugabanninan daga cikinmu su ke fitowa, wajibi ne sai mun gyara kanmu.

Bugu da ƙari, duk irin satar kuɗin jama’a da shugabanninmu suke yi, mu talakawa mu mu ka ba su dama. A yanzu da mutum zai riƙe muƙamin Gwamna ko shugaban ƙaramar hukuma kuma ya sauka ba shi da naira miliyan 100 misali ko kuma ya sauka ya cigaba da rayuwar da ya saba da ita kafin yan hau muƙamin, sai ka ji ana zaginsa ana cewa ba shi da ƙashin arziki. Ko muna tsammanin ma su riƙe da muƙaman ba su san wannan ba? Mu tuna fa cewa, idan zaɓe ya zo, masu mulki ne da masu neman mulki suke zagayawa su na raba mana cin hanci don mu zaɓe su. Wasu daga cikinmu ma har yawo suke yi da ganye a ka, wai su na sayarwa ne.

Wai meye cin hanci ne? Cin hanci shi ne duk wani abu da za’a ba ka na kuɗi ko na amfani wanda zai sa ka ka yi abin da ba shi ya kamata a yi ba a wannan muhallin.

Mu ɗinnan ne fa mu ke taruwa a gidaje da ofisoshin masu mulki mu na tilasta mu su su bamu kuɗi duk da cewa mun san cewa albashinsu bai kai su bamu abinda mu ke nema a gurinsu ba. To tsammaninmu a waɗanne kuɗaɗen su ke ɗebowa su na bamu?

A cikin wannan al’aumma tamu ne, ba’a ganin mutunci ko darajar mutum akan iliminsa, gaskiyarsa ko iya mu’amalarsa, sai dai akan kuɗinsa kuma ba tare da anyi duba da hanyar da ya bi ya samu waɗannan kuɗin ba.

Mu tuna fa mutum ne zai saci kuɗin mutane, amma sai ka ga ya fito ana kwanciya ana gaida shi. A nan garin ne wani ya yi zaman kurkuku na kusan shekaru biyu saboda kotu ta yanke masa hukuncin cewa ya saci kuɗin jama’a. Amma ranar da ya fito, sai da talakawa suka yi gangamin taron tarbarsa da kuma girmamashi. To anan wanene ya ke ɗaurewa cin hanci gindi, mu ne ko kuwa shugabanninmu?

Don haka ko shakka babu, amsata ita ce, mu talakawa mu muke da kaso mafi tsoka wajen hana cin hanci da rashawa a Najeriya duk da cewa su ma shugabannin akwai rawar da za su taka ba ƙarama ba.

Duk mai tunanin gyara a Najeriya, ya fara kallon kansa tsaf, ya ga shi a gyare ya ke? Mutum ya gyara kansa, ya yi gaskiya akan kansa, sannan sai ya yi ƙoƙarin gyara gidansa. Idan ya gama da gidansa, sai ya fara tunanin gyaran unguwarsu, sannan ƙaramar hukumarsu, sannan jiharsa, kafin ya fara tunanin Najeriya.

Cin hanci da rashawa da sata ba za su taɓa rabuwa da mu ba, sai mun yi gaskiya a kasuwancinmu, aikinmu, iyalinmu, ƙungiyoyinmu, abotarmu, Masarautunmu da dukkan al’amuranmu.

Bayan mun yi wannan, sai mu kalli shugabanninmu ido da ido, mu ci kwalar rigarsu, ƙila ma har da lakace mu su hanci sannan mu ce mu su: me ya sa ba ku da gaskiya?

©2013: abdulazeezamir@hotmail.com

No comments:

Post a Comment